Hudubar Bankwana

Ya ku mutane!
Ku saurari maganata da kyau.
Ban sani ba, wata kila bayan wannan shekara ba zan sake haduwa da ku a nan har abada ba.
Ya ku Mutane!
Kamar yadda ranar Arafah take mai tsarki, kamar yadda watan Zulhijjah yake mai tsarki, kamar yadda birnin Makka yake mai albarka; rayukanku, dukiyoyinku, da mutuncinku suma haka suke masu tsarki, amintattu daga kowanne irin hari.
Ya Sahabbaina!
Gobe za ku hadu da Ubangijinku kuma za a tambaye ku game da dukkan ayyukanku na yau. Kada ku koma zuwa ga jahilci bayan tafiyata, ku kashe juna. Wadanda ke nan su isar da wannan wasiyya ga wadanda ba su nan. Wata kila wanda aka isar masa, ya fi wanda ya ji a nan fahimta da kiyaye ta.
Ya Sahabbaina!
Duk wanda ke da amanar wani, ya mayar da ita ga mai ita.
Dukkan nau'in riba an soke su, suna karkashin tafin kafata.
Amma dole ne ku biya asalin bashinku. Kada ku zalunta, kada a zalunce ku.
Da umarnin Allah, ribar yanzu haramun ce. Kowanne irin mummunan al'adar jahiliyya game da riba yana karkashin tafin kafata. Ribar farko da na soke ita ce ta Abbas ɗan Abdulmuttalib.
Ya Sahabbaina!
Dukkan ramuwar gayya na jahiliyya an soke su. Farkon ramuwar gayya da na soke ita ce ta Rabia jikan Abdulmuttalib.
Ya ku Mutane!
A yau shaidan ya rasa ikon tasiri da mulki a cikin wannan ƙasarku har abada. Amma idan kuka bi shi a cikin kananan abubuwan da kuka raina banda waɗanda na soke, hakan zai faranta masa rai. Ku kiyaye wadannan don kare addininku.
Ya ku Mutane!
Ina ba ku shawara da ku kula da hakkokin mata kuma ku ji tsoron Allah a wannan lamari. Kun karbi mata a matsayin amana daga Allah; kun halatta musu mutuncinsu da tsarkin su da alkawarin Allah. Kuna da hakki a kansu, su ma suna da hakki a kanku. Hakkin ku a kansu shi ne kada su bar wani da ba ku yarda da shi ya shiga gidajenku. Hakkin su a kanku shi ne ku ciyar da su da tufatar da su bisa al'ada.
Ya ku Muminai!
Na bar muku amana biyu, muddin kun rike su da kyau ba za ku bace ba. Wadannan amanan su ne Littafin Allah Alkur'ani Mai Girma da Sunnah na Annabi.
Ya ku Muminai!
Ku saurari maganata da kyau kuma ku kiyaye ta da kyau! Musulmi dan'uwansa ne ga Musulmi, kuma dukkan Musulmai 'yan'uwa ne. Haramun ne ku ci hakkin dan'uwanku na addini. Sai dai idan ya yarda da zuciya daya.
Ya Sahabbaina!
Kada ku zalunci kanku. Nafsinku ma yana da hakki a kanku.
Ya ku Mutane!
Ubangijinku daya ne. Mahaifinku daya ne. Dukkanku 'ya'yan Adamu ne, Adamu kuma daga ƙasa ne. Babu fifiko ga Balarabe akan wanda ba Balarabe ba, haka ma wanda ba Balarabe ba akan Balarabe. Babu fifiko ga ja akan baki, ko baki akan ja. Fifiko yana cikin tsoron Allah. Mafi daraja a wurin Allah shi ne mafi tsoronSa.
Ya ku mutane!
Allah Madaukaki ya baiwa kowane mai hakki hakkinsa. Kowa da abin da ya aikata ne zai dauka. Uba ba zai dauki laifin ɗansa ba, ɗansa ma ba zai dauki laifin uba ba.
Ku kula! Kada ku aikata wadannan abubuwa guda hudu:
Kada ku hada wani da Allah.
Kada ku kashe rai da Allah ya haramta sai da hakki.
Kada ku yi zina.
Kada ku yi sata.
Ya ku mutane!
Gobe za a tambaye ni game da ku. Me za ku ce?
Sahabbai suka amsa:
"Mun shaida cewa ka isar da sakon Allah; ka cika aikin manzanci, ka yi mana wasiyya da nasiha."
Manzon Allah ya daga yatsan shaidarsa zuwa sama sau uku
"Ka shaida! ya Ubangiji!
Ka shaida! ya Ubangiji!
Ka shaida! ya Ubangiji!"
Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)